1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya da Kamaru za su yi musayar bayanan sirri

Zainab Mohammed AbubakarJuly 30, 2015

Shugaba Buhari na Najeriya ya kammala ziyarar aiki na yini biyu da ya kai Kamaru, tare da cimma matsaya da takwaransa Paul Biya kan yadda za su yaki Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1G7XP
Präsident von Nigeria Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Najeriya da Kamaru sun bayyana aniyarsu na tsaurara hadin kai a bangaren soji domin domin yakar kungiyar Boko Haram da ta zama gagarabadau a yankin tabkin Chadi. Shugaba Paul Biya na Kamaru ya ce bai kamata wannan annoba ta samu nasarar yaduwa ta ko'ina ba.

Ya yi wannan furucin ne bayan ganawar hadin gwiwa na kwanaki biyu da ya yi da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari, a fadar gwamnati da ke birnin Yaounde. Shugabannin biyu kasashen biyu da ke makwabtaka da juna kuma ke fama da barazanar kungiyar ta Boko Haram, sun lashi takobin musayar bayanan sirri tare da fadada tsaro kan iyakokin kasashen da ke yankin Yammacin Afirka.

Kamerun Präsidenten Paul Biya & Muhammadu Buhari Nigeria
Hoto: Getty Images/AFP/R. Kaze

Wannan dai iata ce ziyarar aiki na farko da shugaban Najeriya ya kai zuwa Kamarun tun bayan daya lashe zabe a watan Maris na wannan shekara, inda ya yi alkawarin shawo kan matsalar ta'addanci da rashin tsaro da kasarsa ke fuskanta na tsawon lokaci.

Boko Haram da ke hankoran kafa daular musulunci domin aiwatar da dokar shari'a kamar yadda suka ce, ta kashe mutane sama da dubu 14, tun daga shekara ta 2009 zuwa yanzu. Hare haren kungiyar dai ya bazama zuwa kasashe makwabta kamar Nijar da Chadi da Kamaru. A wannan wata na Yuli dai hare harin kunanar bakin wake na kungiyar ya kashe mutane 60 a yankin arewacin Kamarun.

Daga kasa ana iya sauraron sautin rahotannin wakilanmu na Kamaru da Najeriya Adamou Maimota da Ubale Musa dangane da ziyarar.