1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Buhari zai yi takara a 2019

Gazali Abdou Tasawa
April 12, 2018

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce zai sake tsayawa takara a zaben shekara ta 2019, lamarin da ya sake farfado da muhawarar da ake yi a kasar game da matakin nasa ta la'akari da yawan shekarunsa.

https://p.dw.com/p/2vwKy
Karikatur: Buhari Candidacy
Hoto: DW

Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da wannan aniya tasa ce a taron jam'iyyarsa ta APC da ya gudana a ranar tara ga wannan wata na Afrilun da muke ciki a garin Abuja. Wannan dai ya kawo karshen kila-wa-kala da aka jima ana yi kan batun sake tsayawar ta Buharin ta la'akari da shekarunsa. Kundin tsarin mulkin Najeriya dai ya halatta yin wa'adin mulki na shekaru hurhudu sau biyu, sai dai bai kayyade yawan shekarun 'yan takarar neman shugabancin kasar ba, wanda ke nufin duk da kasancewa yana da shekaru 75 a yanzu, Shugaba Muhammadu Buhari na na da damar sake tsayawa takarar.