1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Binciken rashawa a fadar gwamnati ya dau zafi

April 26, 2017

A yayin da aka shiga mako na biyu na binciken manyan jami'an gwamnatin tarrayar Najeriya biyu, kwamitin binciken ya ce babu gudu ba kuma ja da baya a kokari na tabbatar da gaskiya komai daci.

https://p.dw.com/p/2byP8
Nigeria Wahlkampf Mohammadu Buhari & Yemi Osinbajo
Hoto: picture-alliance/dpa

Babu dai zato ba kuma tsammani yakin cin hanci da rashawa a tarrayar Najeriya ya karkato zuwa  ga bangaren zartarwar kasar inda sakataren gwamnatin kasa Babachir David Lawal da babban jami'in hukumar leke na asiri Ambassador Ayo Oke suka kare tare da fuskantar bincike bayan dakatar dasu a bakin aiki. An dai fada mako na biyu kuma na karshe a binciken tare da gwamnatin kasar tana fadin an yi nisa sannan kuma babu gudu babu jada baya a yakin.

Ministan shari'ar kasar kuma dan kwamitin binciken na jami'an biyu, Abubakar Malami, ya ce sun gana da dama suna kuma nazari mai fadi da nufin tabbatar da laifi ko kuma akasi.

Sakamako na binciken 'yan kwamitin dai zai kafa dan ba ta tabbatar da sahihancin yakin da ya kalli kama da dama a cikin alkalai dama masu takama da yin dokoki na kasar. To sai dai kuma akwai tsoron yiwuwar a kwata cikin karatun da ya kalli wanke sakataren a bangare na gwamnatin kasr can baya. Abin kuma da a cewar ministan ke zaman daban a karatun da ya wanke Babachir Lawal can baya da kuma wanda yake shirin ya gudana a yanzu.

Wani rahoton majalisar dattawa da ya Ambato dakataccen sakataren da bada kwangila ga kamfanonin da yake da alaka da su, da kuma amincewar babban jami'i na leken asirin na mallakar wasu tsabar kudi har Naira miliyan Dubu goma sha biyar dai na zaman ummul aba'isin kafa kwamitin a karkashin mataimakin shugaban kasar da kuma ake sa ran mika rahotonsa a cikin tsakiyar makon gobe.

A fadar Ministan, 'yan kwamitin da ya kai ga titsiye jami'an guda biyu da ragowar wasu da ake kallon na da alaka da batu na kudade, na samun gagarumin ci gaba a kokarin kaiwa ga bankado zahirin al'amari a badakalar da ke nuna irin jan aikin dake gaban kasar. Abin jira a gani dai na zaman sakamako na rahoton da ma tasirinsa cikin yakin dake kara nuna alamun haske ga kasar da ta yi nisa cikin dagwalon na hanci yanzu.