1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bincike game da yakin Boko Haram

Abdourahamane Hassane
August 11, 2017

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai bakwai da ta nada a cikin makon jiya da nufin nazarin rawar da sojojin kasar suka taka a cikin yaki da Boko Haram.

https://p.dw.com/p/2i5QU
Nigeria Symbolbild Armee Soldaten Offiziere
Hoto: picture-alliance/AP Photo/O. Gbemiga

Kwamitin wanda ya kunshi wakilai na kungiyoyin farar hula da alkalai da kuma sojojin, zai kai ga bincika zargin da kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi na cewar sojojin Najeriyar sun take hakkin dan Adam a yakin da suke yi da Boko Haram. Tun farko dai rundunar sojojin Najeriyar ta gudanar da irin wannan bincike wanda a kansa ta wanke sojojin daga zargin da ake yi musu na take hakkin jama'a a yakin na Boko Haram