1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: Bankado ma'aikatan bogi sama da dubu 20

Kamaluddeen SaniFebruary 29, 2016

Ma'aikatar harkokin kudaden Tarayyar Najeriya ta bayyana cewar ta sami nasarar alkinta miliyoyin daloli bayan ta binciko badakalar ma'aikatan bogi sama da dubu 20.

https://p.dw.com/p/1I4Sk
Nigeria Abuja Präsident Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/dpa/W. Krumm

Mai baiwa ma'aikatar harkokin kudaden ta Najeriya shawara Festus Akanbi ya ce bankado wannan almundahanar ga ma'aikatan bogin zai taimaka gaya wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin kasar da ke zama mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrka.

Wanna dai wata nasara ce da manazarta yau da kullun ta fusakar tattalin arziki ke ganin kakkabe ma'aikatan bogi na iya taimakawa kasar wajen takaita kudaden ga harkokin biyan albashi ga ma'aikatan kasar tare da juya su zuwa wasu fannoni na daban don cigaban kasar.

Tuni dai ma'aikatar kudaden Najeriya tace ta tsame ma'aikatan bogin daga jadawalin biyan albashin ma'aikatun kasar.