Najeriya: Babban titin zamani cikin gandun daji
Dajin Ekuri na cikin matsala. Dajin da ke jihar Cross River a kudancin Najeriya na daya daga cikin gandun dajin da suka rage a yankin. Mahukuntan jihar na son gina babban titi na zamani mai layuka shida a cikin dajin.
Zanga-zangar neman hakki
"A karon farko wani ya saurare mu," ta bakin wani mazaunin karamin kauyen na dajin Ekuri ke nan. Babu wani dan jarida daga kafar yada labarai ta kasar waje da ya taba ziyartar su. Gwamnatin jihar Cross River da ke Kudu maso Gabashin Najeriya ta shirya gina wata babbar hanya da za ta bi ta gandun dajin. Mazauna yankin sun damu kan yadda shirin shimifida titin zai shafi gidajensu da kuma rayuwarsu.
Yankin da aka yi watsi da shi
Al'ummar Ekuri na ganin gwamnati ba ta yi musu wani abin a zo a gani ba. Sun gina gadojin da ke sada su da kauyensu da kansu. Ba su da ruwa da wutar lantarki. A cewar mazauna yankin gabanin zabe wani dan siyasa ya ziyarce su da jirgi mai saukar Ungulu, tare da raba musu kudi da kuma yin alkawura. Sai dai tun bayan zaben, ba su kara jin duriyar sa ba.
Kwace musu matsugunansu
Firgicin ya zo ne a sabuwar shekara: A jarida ne mahukuntan jira ta Cross River suka sanar da cewa za su gina babban titin zamani a fadin jihar. Wadanda ke zaune a nisan kilomita 10 daga hagu da kuma kilomita 10 daga dama za su rasa matsugunansu, za kuma a tilasta musu barin yankin.
Babban titin zamani na farko a Najeriya
Babban titin mai nisan kilomita 260, zai hada sabuwar tashar jiragen ruwa da ke Calabar da yankin arewacin Najeriya. Titin mai layi shida da kuma alkawarin inganta hanyar shimfida shi, gwamnatin jihar na fatan titin ya kasance daya daga cikin titunan zamani a nahiyar Afirka. Shirin shimfida hanyar zai lashe biliyoyin nairori. Sai dai babu masaniya kan inda za a samu kudin.
Ana sare bishiyoyi
Tuni aka fara sare bishiyoyi tun ma kafin kasafin kudi da kuma rahoton kididdiga kan muhalli. An kammala rahoton muhalli, sai dai ofishin ma'aikatar muhalli ta kasar da ke Abuja fadar gwamnatin Najeriyar ya ce sare bishiyun ya sabawa dokokin kasa da kasa kan muhalli.
Motocin rusau cikin shiri
Tun gabanin rahoton kiddidigar, ma'aikatar muhalli ke samun karafe-korafe daga masu rajin kare muhalli da kuma mazauna yankin kan illar sare bishiyun. Motocin rusau din sun dakatar da ayyukansu, sai dai suna nan cikin shiri na ci gaba da ga inda suka tsaya a ko wanne lokaci.
Nau'in bishiyu da dabbobi na cikin hadari
Gandun dajin na Ekuri na dauke da nau'in dabbobi daban-daban kamar goggon biri. Gandun dajin da kuma dauke da tsirrai kala-kala har 1,500, kana ya na daya daga cikin yankuna masu nau'in dabbobi da bishiyu da tsirrai daban-daban a duniya.
"Suna boye wani abu"
Odigha Odigha shi ne tsohon shugaban hukumar lura da gandun daji a jihar Cross River. Tare da hadin gwiwar "Coalition for Environment", ya na kokarin dakile ginin babban titin na zamani. Jihar za ta yi amfani da fili sama da hecter 520,000, kaso 25 na fadin jihar baki daya, a cewar Odigha. Ya ce babu wanda ya fada mana dalilin da ya sa suke bukatar wannan fili, suna boye wani abu.
Samun kudi a saukake mai makon ci-gaba?
Wasu masu fafutuka da mazauna yankin na zargin cewa mahukuntan jihar ba wai sun damu ne da shimfida titin ba, akwai wasu muhimman itatuwa masu matukar amfani a gandun dajin. Sun yi imanin cewa mahukuntan na son sare baki daya wadannan itatuwan su sayar da su ga kasashen ketare.
Babu wani dalilin firgici, a cewar gwamnatin jihar
Kwamishiniyar yada labarai ta jihar Rosemary Archibong ta yi watsi da zargin. Ta ce: "Muna shuka bishiyu biyu a madadin duk bishiya guda da muka sare. Sai dai ba ta da wata amsa dangane da dalilin da ya sanya za a kwace kilomita 10 daga kowanne bangare na babban titin zamanin. Ta ce: "Mutanen da ke zaune a kusa da babban titin ne za su ci moriyar ci-gaban, misali noma. Har yanzu muna tattaunawa."
Ci gaba da nuna kin amincewa
Babu wanda ya tambaye mu, a cewar mazauna yankin Ekuri. Margret Ikimu ta ce gwamnati ta ba ta kunya. Ta ce: "Kamata ya yi su fara gyara titunan da muke da su." "Gwamnatin na kan karagar mulki tsawon shekara guda, amma har yanzu babu wani abu da ya sauya ta fuskacin inganta rayuwa. Yanzu suna son karbe mana dan abin da muka mallaka, wannan gandun dajin."