Najeriya ba ta cikin haramcin shiga Amirka | Labarai | DW | 09.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya ba ta cikin haramcin shiga Amirka

Ofishin jakadancin kasar Amirka a Najeriya ya sanar cewa, matakin da Amirka ta dauka kan siyasarta ta 'yan gudun hijira bai shafi Tarayyar Najeriya ba.

Ofishin Jakadancin na Amirka ya fitar da wannan sanarwa ce a matsayin martani kan wata sanarwar da ka iya hana 'yan Najeriya samun kwarin gwiwa na zuwa kasar ta Amirka. Sanarwar ta Ofishin jakardancin ta ce babu wani dalili, idan har dan Najeriya ya samu takardun izinin shiga kasar a ce ba zai shiga ba, domin babu wani hani da ya shafi 'yan Najeriya zuwa Amirka.

A ranar Litinin da ta gabata ne dai, mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin diflomasiyya Abike Dabiri-Erewa, cikin wata sanarwa ta ce, ya kyautu 'yan Najeriya da ba su da kwararan dalillai na zuwa Amirka su dage bulaguronsu zuwa wannan kasa, inda ta ce a 'yan makonnin baya-bayan nan, sun samu labarin cewa an dawo da wasu daga cikin 'yan Najeriya masu bukatar zuwa kasar ta Amirka duk kuwa da cewa suna da takardun izini shiga kasar.