1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An yi awon gaba da sandar majalisar dattawa

Ramatu Garba Baba
April 18, 2018

Wasu mutane uku da ba'a san ko su waye ba sun kutsa zauren majalisar dattawa ta kasar inda suka yi awon gaba da sandar Majalisar.

https://p.dw.com/p/2wGR1
Nationalversammlung in Abuja, Nigeria
Hoto: cc-by-sa/Shiraz Chakera

Wani wanda al'amarin ya faru a kan idonsa ya shedawa kamfanin dillancin labaran Reuters cewa, ya na kallo mutanen uku suka shiga zauren majalisar suka kuma yi awon gaba da sandar a cikin dan kankanin lokaci. Mai magana da yawun majalisar Aliyu Sabi Abdullahi ya baiyana lamarin a matsayin laifin cin amanar kasa, Kawo yanzu ba a iya tantance mutanen ba da kuma dalilinsu na yin hakan. Bisa dokokin kasar, majalisar ba ta da hurumin aiwatar da doka ba tare da wannan sandar ba.