1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: An sace 'yan mata a Yobe

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 22, 2018

A Najeriya wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun sace 'yan mata sama da 90 a jihar Yobe da ke yankin Arewa maso Gabaashin kasar da kuma da ke fama da hare-haren ta'addanci.

https://p.dw.com/p/2t9md
Nigeria Boko Haram Terrorist
Mayakan Boko Haram da suka addabi Najeriya da makwabtantaHoto: picture alliance/AP Photo

Duk da cewa gwamnatin Tarayyar Najeriyar ta musanta zancen sace 'yan matan 'yan makarantar sakandare a jihar Yobe, sai dai mahukuntan jihar ta Yobe sun sanar da cewa jami'an tsaro sun fafata da mayakan na Boko Haram tare da ceto wasu daga cikin 'yan matan. A baya dai gwamnatin Tarayya Najeriya ta nunar da cewa sojojin kasar na samun nasara a yakin da suke da mayakan na Boko Haram da suka addabi Najeriyar dama wasu makwabtanta.