1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Najeriya: An dakile harin kunar bakin wake

Hukumomin tsaro a Najeriya sun yi nasarar dakile yunkuirin wasu mata biyu na kai harin kunar bakin wake a Maiduguri da ke arewa maso gabashin kasar.

Yan sanda a Najeriya sun ceto rayuwar wata matashiya dauke da jigidan bama bamai yayin da kuma suka harbe wata yar kunar bakin waken. Suka ce matan biyu sun yi shirin kai hari ne birnin Maiduguri a arewa maso gabashin kasar.

Kakakin yan sandan Victor Isuku yace sojoji da ke aikin sintiri sun hango matan biyu sun dumfari wani wurin makamashin gas, yayin da aka bukaci su tsaya sai suka ki suka ci gaba da tafiya.

Ganin haka sai sojojin suka harbe daya daga cikin matan yayin da dayar kuma ta yi saranda.

Kakakin yan sandan yace dukkan matan suna sanye da rigar bama bamai kuma sojojin sun sami damar kwance bama baman..

Lamarin dai ya auku ne a ranar Talatar nan a wajen Maiduguri.