1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

jeriya, Afirka Ta Kudu, Sudan

Bashir, AbbaMay 28, 2008

Halin da ake ciki a Afirka Ta Kudu

https://p.dw.com/p/E7fY
Farautar baƙi a Afirka Ta KuduHoto: picture-alliance/ dpa

Babban abin da ya fi daukar hankalin jaridu da mujallun Jamus dangane da al'amuran Afurka a wannan makon shi ne hare-haren da ake kai wa kan baƙi a Afurka ta Kudu. Amma da farko zamu fara ne da wani rahoton da jaridar kasuwanci ta Handelsblatt ta rubuta a game da wata yarjejeniyar samar da wutar lantarki da kamfanin General Electric ya ƙulla da Nijeriya, wadda ta ƙunshi miliyoyi na dalar Amurka, amma fa har yau babu wani kwan fitila ɗaya dake cin gajiyar wannan yarjejeniya. Jaridar ta ci gaba da bayani tana mai cewar:

“A kullun safiya idan garin Allah ya waye sai masu tsaron tashar jiragen ruwan Koko ta kudancin Nijeriya sun bayyana mamakinsu a game da wasu manyan injuna na lantarki da aka ɗora musu alhakin tsaronsu yau tsawon watanni da dama amma ba wanda ya ranar da za a kwashesu daga wurin. Alƙaluma sun nuna cewar a jiya da kuma tsaron waɗannan injuna kawo yanzu sun cinye abin da ya kai Euro miliyan talatin, wato kwatankwacin Naira miliyan dubu hudu da ɗari takwas, kuma ba wani takamaiman shiri ko ranar da aka tsayar domin kwashesu daga tashar Koko domin kai su wuraren da za a yi amfani da su a ƙuryar kasar Nijeriya.”

A kwanakin baya-bayan nan an wayi gari baƙar fatar Afurka ta Kudu na farautar ‘yan uwansu baƙar fata dake neman mafaka a ƙasar suna masu yi musu kisan kiyashi, lamarin da ya kaɗa zukatan dukkan ‘yan Afurka da ma na wasu sassan duniya daban. Jaridar Süddeutsche Zeitun ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Dubban ‘yan gudu hijira suka runtuma domin neman mafaka a coci-coci da tashoshin ‘yan sanda domin kare makomar rayuwarsu daga ‘yan banga dake ta da zaune tsaye a yankunan baƙar fatar Afurka ta Kudu. Masu alhakin wannan ɗanyen aiki, hankalinsu ya fi karkata ne kan ‘yan ƙasar Zimbabwe su kimanin miliyan uku da suka tsere zuwa Afurka ta Kudun domin gudun ɗanyen mulkin shugaba Robert Mugabe. Amma abin takaici a nan shi ne, a zamanin baya lokacin da baƙar fatar Afurka ta Kudu ke fama da raɗaɗin mulkin wariyar jinsi, kawayenta na Afurka sun tashi haiƙan wajen taimaka mata a fafutukar ‘yantar da kanta daga wannan danniya da kama karya. Ta la'akari da haka wannan matakin ya zama tamkar cin amanar ‘yan uwansu da suka taimaka musu.”

Ita kuwa jaridar Die Zeit a cikin nata sharhin nuni tayi da cewar:

“Kafa wani kwamitin bincike domin bin diddigin musabbabin farmakin da baƙar fatar Afurka ta Kudu ke kaiwa kan ‘yan-uwansu baƙar fata dake neman mafaka a ƙasar ba zai tsinana kome ba. Domin kuwa ba kome ba ne dalilin waɗannan tashe-tashen hankula illa gazawar gwamnati wajen kyautata makomar rayuwar baƙar fata masu rinjaye a ƙasar, inda yawancinsu ma suka gwammace jiya da yau.”

Ita ma jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi akan wannan ta'asa tana mai cewar:

“Abin dake faruwa a Afurka ta Kudu na mai yin nuni ne da cewar wariyar jinsi ba ta da wata nasaba da launin fata. An fuskanci ire-iren wannan ta'asa a Ruwanda da Bosniya, inda masu alhakin kisan kiyashin zasu mayar da maƙobtansu saniyar ware domin samun ƙarfin zuciyar kai musu hari. A sakamakon haka aka kirkiro mummunar kalman nan ta tsaftace ƙabila.”

A wannan makon jaridar Financial Times Deutschland ta mayar da hankalinta ne akan sabuwar rawayr da ƙasar Japan ke fafutukar takawa a nahiyar Afurka a gasa da ƙasar China, inda ta riɓanya yawan kuɗaɗen taimakon raya ƙasa da take ba wa ƙasashen nahiyar. Jaridar ta ce manufar Japan a game da wannan shiri shi ne sake farfaɗo da matsayinta da tayi asararsa a tserereniyar ɗora hannu kan albarkatun ƙasa a Afurka. Dangane da su kansu kasashen Afurka kuwa wannan gasa zata kai su gaba, saboda sata ba su wani kyakkyawan matsayi a yarjeniyoyin da zasu ƙulla nan gaba.”