n tara kudaden yaki da cutar masassarar tsuntsaye | Labarai | DW | 18.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

n tara kudaden yaki da cutar masassarar tsuntsaye

Mahalatta taron kasa da kasa akan masassarar tsuntsaye a China sun tabbbatar da cewa an sami dala miliyan dubu daya da miliyan dubu dari biyar don yakin cutar a duniya.

Saidai Kwamishinan lafiya na kungiyar gamayyar turai Markos Kiprianou wanda ya sanarda hakan yace matalautan kasashenen kudu maso gabashin Asia da Afrika ne zasu sami taimako daga kudaden da aka tara.

Tun farko dai babban sakataren majalisar dinkin duniya Kofi Annan yayi kira ga kasashen duniya dasu gaggauta daukan matakin shawo kan annobar masassarar tsuntsayen .

Daga cikin Jimillar kudin kungiyar gamayyar turai tayi alkawarin bayarda kusan dala miliyan maitan da hamsin.

Kawo yanzu dai akalla mutane dari da hamsinne suka kamu da cutar a kasashe shida galibinsu a kudu maso gabashin Asia, kuma akalla mutane 79 ne cutar ta hallaka tun daga shekara ta 2003.