Myanmar: Bukatar yin hukunci kan fyade | Labarai | DW | 06.02.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Myanmar: Bukatar yin hukunci kan fyade

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayyana bukatar da ke akwai ta hukunta manyan jami'an tsaron kasar in har suka bari aka cigaba da yi wa mata na kabilar Rohingya cin zarafi ta hanyar lalata.

A wani bincike da kungiyar ta gudanar ta ce anci zarafin mata da damar gaske wasunsu ma shekarunsu ba su gaza 13 ba kuma a wasu lokutan maza da yawa ne kan afkawa mace guda don tursasa mata wajen yi lalata da ita. Wannan ne ya sanya Human Rights Watch din jan hankalin hukumomin kasar wajen ganin sun dau mataki na kare 'yan kabilar ta Rohingya wandan musulmi ne kuma suke cikin tsirarun kabilun kasar.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Myanmar din ba ta kai ga cewa uffan ba dangane da wannan bukata da aka mika maika mata amma kuma rahotanni na cewar 'yan kabilar ta Rohingya na cigaba da ficewa daga kasar don neman mafaka a kasashe makota musamman ma Bangladesh.