Mya’aikatar tsaron Iraqi ta tabbatar da mutuwar wasu dakarun Amirka guda biyu, waɗanda tun ran juma’a ne aka rasa ɗuriyarsu. | Labarai | DW | 21.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mya’aikatar tsaron Iraqi ta tabbatar da mutuwar wasu dakarun Amirka guda biyu, waɗanda tun ran juma’a ne aka rasa ɗuriyarsu.

Ma’aikatar tsaron Iraqi ta tabbatad da mutuwar wasu sojojin Amirka guda biyu, waɗanda tun ran juma’a ne aka ba da sanarwar ɓacewarsu a kudancin birnin Bagadaza. Jami’an gwamnatin ƙasar, sun ce, alamun da aka gano kan gawawwakin sojojin guda biyu na nuna cewa, an yi musu matuƙar azaba. Tun ɓacewar sojojin ne dai aka tarwatsa dubban dakarun Amirka zuwa nemansu.

Wata ƙungiya da ke da jiɓinta da ƙungiyar al-Qaeda a Iraqin, wadda ta yi ikirarin yin garkuwa da sojojin biyu, ta kuma ce ita ta kashe su. A halin da ake ciki dai, dakarun Amirkan sun ce sun kashe wasu ’yan tawayen Iraqin guda 15, a wani harin da suka kai kan wata gonar dabbobi a cikin daren jiya, kusa da garin Baquba, da ke arewa maso gabashin Bagadaza. Amma ’yan uwan waɗanda aka kashen da kuma ’yan sandan garin, sun ce duk waɗanda Amirkawan suka kashe ma’aikatan wata gonar kaji ne.