1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutuwar mata lokacin aihuwa ta ja baya a duniya

Gazali AbbdouTasawaNovember 12, 2015

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya ta WHO ta wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewar matsalar mace-macen mata a lokutan haihuwa ta ragu da kusan kishi 50 cikin dari a shekaru 25 na baya-baya nan.

https://p.dw.com/p/1H4bx
Zwillinge am 11.11.2011 geboren
Hoto: picture alliance / dpa

Wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ,ko kuma OMS ta wallafa a wannan Alhamis ya nunar da cewar matsalar mace- macen mata da ake samu wajen aihuwa a duniya ta ragu da kusan kashi 50 cikin dari a cikin shekaru 25 na baya-bayan nan.

Rahoton ya ce nan zuwa karshen wannan shekara ta 2015 mace-macen mata a lokacin aihuwa zai ja baya da kishi 44 daga cikin dari idan aka kwatanta da alkalumman shekara ta 1990.

Amma rahoton ya ce kasashe tara ne kawai da suka hada da Cape-Verde da Kambodiya da Iran da Ruwanda suka cimma wannan buri na rage mace-macen mata a wajan aihuwa da kishi ukku daga cikin hudu wanda ke daya daga cikin muradai takwas na wannan karni da Majalissar Dinkin Duniya ke son cimma nan zuwa karshen wannan shekara ta 2015.

Sai dai Hukumar ta WHO ta ce akwai babbar tazara tsakanin kasashe a ci gaban da aka samu a wannan fanni inda kishi 99 daga cikin dari na mace-macen matan da aka fuskanta a lokuta aihuwar ya wakana ne a a kasashe masu tasowa