Mutuwar ma′aikata 105 sakamakon fashewar bututun gas a kasar Sin | Labarai | DW | 07.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar ma'aikata 105 sakamakon fashewar bututun gas a kasar Sin

Yawan ma’aikata da suka mutu sakamakon wani haɗarin fashewar bututun gas da ya auku a wata ma’aikatar haƙar kwal dake arewacin ƙasar Sin ya haura zuwa 105. Da yawa daga cikin waɗanda haɗarin ya rutsa da su, sun mutu sakamakon shaƙar iskan gas mai cike da guba. Majiyar ‚yan sanda, tace har yanzu dai ana cigaba da kai taimako. Jami’an tsaro sun kama shugabannin ma’aikatar kann zargin jinkirta kiran taimako daga hukuma, har sai bayan awa shida da aukuwar wannan haɗari. Ana kyautata zaton cewar ma’aikatar na anfani da ma’aikata da basu da izinin aiki wajen gudanar da aikace aikace a ma’aikatar dake ƙarƙashin ƙasa.