1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya

Jakadan Rasha mafi dadewa a Majalisar Dinkin Duniya ya mutu ne a yau a birnin New York na Amirka.

Russischer UN-Botschafter Witali Iwanowitsch Tschurkin (picture-alliance/abaca/B. Samsas)

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya

Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Rasha,ta sanar da mutuwar jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin. Rahotanni sun nunar da cewa Churkin wanda ya kasance jakadan na Moscow mafi dadewa a Majalisar ta Dinkin Duniya ya mutu ne a yau a birnin New York na Amirka. Kawo yanzu dai babu cikakken rahoto dangane da sanadiyyar mutuwar tasa, sai dai alamu na nuni da cewa mutuwar tasa ta ta kasance ta bazata.