Mutuwar Abu Sayyaf | Labarai | DW | 20.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutuwar Abu Sayyaf

Gwamnatin kasar Phillipinne ta ba da tabbacin mutuwar shugaban kungiyar ta’addan kasar ta Abu Sayyaf. Wani mai magana da yawun gwamnatin ya ce binciken da jami’an Amurka suka gudanar akan wata gawar da aka gano watan da ya gabata ya tabbatar cewar ta Khaddafy Janjalani ce, wanda aka sanya lada ta dala miliyan biyar akansa. An kashe shi ne a lokacin wata ba ta kashi tare da sojojin Philippine watan satumban da ya wuce. Wannan rahoton ya zo ne kwanaki kadan bayan da sojan Philippine suka kashe Abu Sulaiman daya daga cikin kwamandojin dakarun kungiyar ta Abu Sayyaf a tsuburin Jolo. Ana dai kyautata zaton cewar kungiyar tana da alaka da ta al-ka’ida