Mutumin da zai gaji babban sakataren Kofi Annan | Labarai | DW | 23.06.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutumin da zai gaji babban sakataren Kofi Annan

Rahotanni sun ce kasar Indiya zata gabatar da mataimakin babban sakataren MDD Shashi Tharoor a matsayin mutumin da zai gaji Kofi Annan. A karshen wannan shekara wa´adin aiki na biyu na mista Annan ya ke karewa. A cikin shekara ta 1978 Tharoor ya fara aiki da MDD. Kuma a halin yanzu shi ke shugabantar bangaren yada labaru na majalisar. Ita kuwa kasar Sin wadda a cikin watan afrilu ta karbi jan ragamar shugabancin kwamitin sulhu, ta fi son a bawa wani dan nahiyar Asiya wannan mukami na babban sakataren MDD. Kawo yanzu dai ministan harkokin wajen KTK Ban Ki Moon da mukaddashin FM Tahiland Surakiart Sathirathai da kuma dan diplomasiyan kasar Sri Lanka Jayantha Dhanapala zasu iya takara a wannan mukami.