1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutum biyu sun rasu sakamakon artabun da aka yi a Kongo

An harbe akalla fararen hula biyu har lahira a musayar wuta da aka yi yau asabar tsakanin sojoji sa kai masu biyayya da ´yan takarar shugaban kasar JDK. ´Yan sanda a birnin Kinshasa sun ce an yi arangama tsakanin magoya bayan shugaban kasa Josef Kabila da mataimakisa kuma babban abokin hamaiyarsa Jean-Pierre Bemba. Tashin hankali ya barke ne a lokacin da ´yan Kongo ke zaman jirar sakamakon zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar a ranar 29 ga watan oktoba, inda aka yi takara tsakanin Kabila da Bemba. Daga yanzu zuwa ranar 19 ga watannan na nuwamba ake sa ran samun sakamakon karshe na zaben.