Mutum biyu sun mutu a hari da wuka a kasar Finland
August 18, 2017Talla
A kasar Finland mutum biyu sun mutu wasu shida sun sami rauni a wani hari da aka kai da wuka a kan jama'a, abinda ya sa hukumomi karfafa tsaro a duk sassan kasar, al'amarin ya auku ne a wannan juma'a a birnin Turku da ke yammancin kasar, shugaban kasar Sauli Niinisto ya halaci taron gudanar da addu'oi ga wadanda suka rasa rayukansu.
A sanarwar da ma'aikatar tsaron kasar ta fitar ta ce 'yan sanda sun yi nasarar harbe daya daga cikin maharan a yayin da ake ci gaba da farautar sauran da suka tsere wa jami'an tsaro. Kawo yanzu dai wadanda suka jikkata na samun sauki a asibiti, ba a kuma kai ga tantance ainihin dalilin kai harin ba, ko kuma ya na da nasaba da harin ta'addanci.