Mutane talatin sun mutu a wani hari a Iraqi | Labarai | DW | 04.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane talatin sun mutu a wani hari a Iraqi

Iraq/Funeral

A Iraq kalla mutane talatinne suka rasa rayukansu da dama kuma suka jikkata a wani hari da aka kaiwa wasu yan shia yayin wata janaiza a wata makabarta.

Yansanda sunce wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam din dake jikinsa adai dai lokacinda masu janaizar kusan su dari da suke binne gawar danuwan wani dan siyasa na yankin da ya rasa ransa a wani hari ,bayanda shima dansiyasar ya tsallake rijiya da baya jiya a kokarin kashe shi da akayi.

Harindai ya farune a garin Muqadiyya dake da tazarar Kilomita kusan casain daga Bagadaza.

Kafin wannan harin ma wasu mutane uku ne suma suka mutu akalla wasu goma sha uku kuma suka raunana a wani harin bam da aka dana a mota a Bagadaza.

Wani da ya ga yadda lamarin ya auku yace da alamu anyi nufin kai harinne akan wasu motocin yansanda biyu da suke wucewa ta wurin a dai dai lokacin da bam din ya fashe.

Harin dai ya wakana ne yayinda ake kara tsaurara tsaro a Bagadazan bayanda a jiya aka sace yar uwar ministan cikin gidan Iraqin.