1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sun rasa rayuka a Indonesia a sakamakon rugujewar gina

Gwamnatin Indonesia ta sanar cewar akalla mutane 3 suka rasa rayukan su inda dalar datti ta rufe wasu 20 da ransu a lokacin da wani ginin da ake jibge dattin ya rushe a babban birnin Jakarta. Rahotanni sunce daruruwan mutane masu tsintar dukiya na kann saman dalar dattin, a lokacin da hadarin ya auku. Daruruwan mutane a kasar, na dogaro da yawan kayan da suke tsinta wadanda suka hada da robobi da jikkunan leda kana da itacen timba domin rayuwa. A watan febrairun shekarar 2005, sai da mutane 140 suka rasa rayukan su a lokacin da kasar ta fuskanci wani zaizayar kasa.