Mutane sun hallaka a wani harin kunar bakin wake a birnin Mogadishu | Labarai | DW | 09.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sun hallaka a wani harin kunar bakin wake a birnin Mogadishu

Akalla mutane uku suka rasu a wani harin kunar bakin wake da aka kai kan shalkwatar 'yan sandan Somaliya da ke birnin Mogadishu.

Wani dan harin kunar bakin wake a mota ya kai hari a gaban harabar shalkwatar 'yan sandan Somaliya da ke Mogadishu babban birnin kasar, inda ya halaka mutane hudu sannan ya jikata jami'an 'yan sanda tara. 'Yan sanda biyu na daga ciki wadanda suka rasu sannan an harbe 'yan tarzoma biyu har lahira wadanda suka yi kokarin farma harabar 'yan sandan kula da harkokin sufuri da ke a unguwar Abdi-Aziz. Said Ahmed Said shi ne kwamishinan 'yan sandan lardin Shangani wurin da aka kai harin ya yi karin bayani.

"Wani mummunan abu ya faru a nan kuma abin da zan ce shi ne Allah Ya halicce mu, kuma a gareshi za mu koma. Akalla mutane uku aka kashe sannan wasu uku sun jikata. Ina kira ga jama'a da su zama masu lura nan gaba."

Tuni dai kungiyar al-Shabab ta dauki alhakin kai harin da ya kawo karshen tsawon lokaci na kwanciyar hankali a yankin da ke kusa da gabar teku.