1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane sun bace a karkashin kasa a Myanmar

Salissou BoukariDecember 26, 2015

Sakamakon wata girgizar kasa mutane da dama sun bace a wannan Asabar din a wata mahakar ma'adanai da ke Arewacin Myanmar .

https://p.dw.com/p/1HTvR
Hoto: Reuters/D. Sagolj

Da yake magana da kanfanin dillancin labaran kasar Faransa na AFP, daya daga cikin ma'aikatan yankin, ya ce a halin yanzu dai masu aikin ceto sun fara aikin nemo gawarwaki kuma ba za su iya bayar da wani adadi ba a yanzu. A karshen watan Nuwamba ma dai a kalla mutane 100 ne suka rasu a iri-irin wannan hadari na motsawar kasa a wani yanki mai nisa na kasar da ke iyaka da kasar Sin bayan da wani dutsi ya ragargaje bisa wasu gidaje yayin da mutane ke cikin barci a daidai lokacin.