1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane sama da 40 sun rasa rayukan su a Iraq

Wasu bama bamai biyu sun tashi a cikin wata karamar mota a tsakiyar birnin Bagadaza. Hakan a cewar rahotanni,yayi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 40 ban da wasu da dama da suka jikkata.

Bama baman biyu dai sun tashi ne, a kusa da ofishin daukar sabbin jami´an yan sanda dake birnin na Bagadaza.

Ci gaba da faruwar rikice rikice da tashe tashen hankula a Iraqin, ya haifar shugaba Bush neman taimakon makotan kasashen Iraqin tabbatar da tsaro da kuma oda a kasar.

Wannan kira dai ana kallon sa a matsayin hannun ka mai sanda ne

ga kasashen Syria da kuma Iran.