Mutane miliyan goma ne ke fuskantar barazana a Nahiyar Africa | Labarai | DW | 16.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane miliyan goma ne ke fuskantar barazana a Nahiyar Africa

Hukumar bada tallafin abinci ta Mdd, tace kusan dalar Amurka miliyan 240 ake bukata don tallafawa miliyoyin mutane a nahiyar Africa da abinci a cikin wannan shekara.

A cewar hukumar ta Mdd, a yanzu haka akwai mutane kusan miliyan goma da yunwa takewa barazana a wasu kasashe na yammaci da kuma gabashin nahiyar ta Africa.

Hakan , a cewar hukumar bayar da tallafin abincin , ya biyo bayan matsaloli ne na fara da rashin damina mai kyau da kasashen suka fuskanta a shekarar data gabata.

Ya zuwa yanzu dai a cewar rahotanni, hukumar ta Mdd, ta samu tallafin dalar Amurka miliyan 18 da digo hudu daka cikin dala miliyan 240 da take nema.