Mutane miliyan 16 ne zasu kada kuri´un su a zaben shugaban kasa a Tanzania | Labarai | DW | 13.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane miliyan 16 ne zasu kada kuri´un su a zaben shugaban kasa a Tanzania

Daya daga cikin ja gaban neman shugabancin kasar Tanzania, wato Jakaya Kikwete ya fadi kasa a yayin da yake gabatar da jawabi a gaban daruruwan magoya bayan sa a wani guri dake wajen birnin Dar –russalam.

Jim kadan dai da faduwar tasa, akayi gaba dashi izuwa asibitin birnin don duba lafiyar sa.

Rahotanni da suka iso mana na nuni da cewa Jakaya mai shekaru 55, ya fadi kasan ne a sakamakon tsafi da yayi masa yawa bisa turmutsutsu da cinkoson jama´a.

Awowi kadan bayan tafiya dashi asibitin, sai shugaban kasa mai ci, wato Benjamin Mkapa yace dantakarar su ya fadi ne a sakamakon zafi da kuma kishirya data kama shi, amma yanzu haka ya dawo izuwa cikin hayyacin sa.

Ya zuwa yanzu dai bayanai daga kasar na nuni da cewa, Jakaya Kikwete dake takara karkashin jamiyya mai mulkin kasar,da alama shine zai lashe zaben shugaban kasar da za a gudanar a gobe laraba idan Allah ya kaimu.

Neman wannan mukami dai na Jakaya Kikwete, wanda yanzu haka shine ministan harkokin wajen kasar, ya biyo bayan kasancewa ne na hannun daman Benjamin Mkapa, wanda yake kammala wa´adin shugabancin sa a karo na biyu a jere.