1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane masu shiru-shiru da masu yawan magana

Abba BashirDecember 19, 2005

Wadanne ne suka fi yawa a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVg
Al'umma daya hali ban-ban
Al'umma daya hali ban-banHoto: AP

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum barkammu da wannan lokaci, barkanmu kuma da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku, shirin da ke amsa tambayoyin masu sauraro.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun malam Zaharaddeen Mohammed birnin Algiers a kasar Algeria. Ya ce don Allah ina so ku sanar dani, wai shin tsakanin mutane masu shiru-shiru da kuma masu yawan magana wadanne ne suka fi yawa a duniya?

Amsa: An gudanar da wani shiri domin sanin rukuni na halayya da kuma dabi’un dan adam, wanda aka fi sani da suna (Myers-Briggs Type Indicator) a turance. Shi wannan shiri, shiri ne na musamman da aka gudanar domin sanin aji-aji na hankali dakuma dabi’un dan adam. Kuma a ciki ya kunshi harda cewa ko mutum mai shiru-shiru ne kokuma mai yawan magana ne .

Sakamakon wannan nazari ya nunar da cewa ,sudai mutane masu shiru-shiru suna samun kuzarinsu ne daga kansu da kansu, su kuwa mutane masu yawan magana suna samun kuzari nayin wani motsi kokuma aiki ta hanyar cudanya da wasu .hasashen da yake nuna cewar su mutane masu shiru-shiru suna da jinkunya ko kuma tsoron yin magana a bainar jama’a ba gaskiya bane. Mutum mai shiru shiru zai iya dogaro da kansa kuma ya kasance kodayaushe a cikin shiri na tunkarar abinda ke gabansa

Daga bayanai da dama da muka samu, bincike ya nunar da cewa mutane masu yawan magana su suke da kashi 60-75 bisa dari na yawan al’ummar Duniya, su kuwa mutane masu shiru-shiru aka bar musu sauran kason da bai wuce kashi 25-40 bisa dari na alummar duniya ba. Wannan kididdiga na nuni da cewar mafiya yawan alummar Duniya mutanene da suke da bukatar sai an nusar da su abubuwa an dora su akan turba sannan su bi.

Akwai wani mutum dagacikin rukunin mutane masu shiru-shiru da yayi wani littafi da ya sawa suna “Tsarin danniya na masu yawan magana“ wato (The Tyranny of the Extroverts) a turance, inda ya ke bayyana damuwarsa akan yadda mutane masu kaudi a cikin alumma suke danne mutane masu shiru-shiru, saboda yawan maganar da su masu kaudin maganar suke da shi, da kuma shiru-shirun da su masu shiru-shirun suke da shi. Ammafa duk da haka masu shiru-shiru a cikin alumma bai kamata su damu ba, domoin kuwa duk da cewa an fi su yawa a cikin al'umma, bincike ya tabbatar da cewa kashi 60 bisa dari na yara masu kaifin basira a Duniya suna cikin rukunin mutane masu shiru-shiru ne.