1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

181108 D Pflegefamilien

Mohammad AwalNovember 25, 2008

A cikin shekarun baya-bayan nan an samu ƙaruwar yawan yaran da ake ba da su riƙo ga iyayen aro.

https://p.dw.com/p/G1qw
Tsohon gidan marayu na Yahudawa a BerlinHoto: picture-alliance / Tagesspiegel

Idan iyaye suka kasance ba su da wata mafita wataƙila saboda suna matasa ko saboda rashin haƙuri ko saboda dalilai na rashin lafiya to wani lokacin zaɓi daya ya rage wato ƙwace yaran daga hannunsu. Wasu yaran ana kai su irin gidajen nan ne na marayu yayin da wasu kuma ake sa su hannun iyalai masu renon yara. To shirin Mu Kewaya Turai na wannan makon zai duba wannan batu ne da yanzu yake ƙara bunkasa a nan Jamus.

Alƙalumma sun yi nuni da cewa a kowace rana ofishin kula da matasa a Jamus na bawa yara kimanin 77 mafaka a cibiyoyin da ya tanadar na musamman. Tun kimanin shekaru biyar da suka wuce yawan yaran da ofishin ke kula da su yake ƙaruwa. Rahotannin dake nuni da yawan yaran da ke fama da matsananciyar yunwa a gidajensu da waɗanda iyayensu ke gana musu azaba na ɗaukar hankalin jama´a ƙwarai da gaske. Da yawa daga cikin yaran da ake karɓar renonsu daga hannun iyayensu ana kai su gidajen marayu ne yayin da wasu kuma ake kai su gidajen wasu iyalai ko wasu mutane kamar Marlies Moukhmalschi ke aikin renon ƙananan yara.

“Tambayar farko da za ka yiwa kanka ita ce waɗanne irin yara ne? Ɗaukacinsu suna zuwa ne a cikin mawuyacin hali, ba su da wata tarbiya ta gari. Ba su san iyakarsu ba. Idan ka ga halin da suke ciki wallahi abin tausayawa ne, domin da yawa daga cikinsu a rame ake kawo su, duk sun fita kamanninsu. Saboda haka sai ka yi tunani yaya jariri ko yaro ƙarami a cikin wannan hali zai ji daɗin rayuwarsa.”

Maries Moukmalschi ta naƙalci ire iren abubuwan dake wakana a tsakanin wasu iyalan. Tun kimanin shekaru shida kenan tana aikin kula da yara. A tsawon waɗannan shekaru wannan talika da iyalinta sun ba da mafaka ga yara 17 da suka shiga wani hali. A kullum tana ƙoƙarin bawa yaran kulawa da ta dace wadda ba su samu daga iyayensu ba. Ofishin kula da matasa a na kai mata yaran waɗanda ba su iya zama tare da iyayensu. Kowane yaro na zama tare da ita tsawon watanni shida wato wa´adin da ofishin ke ɗiba na yanke shawara ko za a mayar da yaran ga iyayensu ko kuma a kai su gidajen marayu ko kuma su ci-gaba da zama da masu kula da su har abada.

Marlies Muckmalshi wadda ita kanta uwa ce amma yanzu ´ya´yanta sun girma, tana da ƙwarewa wajen renon yara. To amma yaran da ofishin kula da yara da matasa ke kawo mata suna da wahala wajen reno saboda wahalhalu na rayuwa da suka sha.

“Bai kamata ka fara tunanin irin mawuyacin halin da yaro ya kasance a ciki ba. Ba zan taɓa tunanin cewa iyaye za su iya yiwa ´ya´yan cikinsu wannan abu ba. An taɓa kawo min wani yaro mai watanni uku da haihuwa wanda aka sha kwantar da shi asibiti saboda karaya a haƙarƙarinsa da hancinsa, hatta hannun hagunsa ya karye ga kuma kumburi a jikinsa saboda kwanciyar jini. A nan dole kenan ka nuna masa ƙauna da ba shi kulawa da ta dace.”

Jarirai da yaran makaranta wani lokacin ma ´yan´uwan juna daga iyalai na Jamusawa da Turkawa wani lokaci ma daga Afirka ta Kudu, Marlies Muckmalschi da mijinta suna kula da su musamman kasancewar ita Marlies ta iya yarurruka masu yawa ciki har da Ingilishi da Italiyanci da kuma Faransanci. Hakan na matsayin wata fa´ida musamman idan iyayen yaran baƙi ne waɗanda ba su iya Jamusanci sosai ba. To amma me ya sa ta ke wannan aiki? Marlies cewa ta yi.

“´Ya´yana duka sun girma kuma ba na ma son sake haihuwa. Haka kuma ba mu da ƙarfin ɗauko yara daga kasashe masu tasowa. Saboda haka mu ka yi tunani muka ga cewa da akwai damar taimakawa yara na kurkusa da mu domin a nan Jamus ma ai akwai yaran da iyayensu ba su da ƙarfi kuma suke matuƙar buƙatar taimako.“

Da yake sau da yawa hukumomin dake kula da harkokin matasa na yawaita ƙwato yara daga iyalansu, ya sa a dole suke neman iyalan da ke da sha´awar ɗaukar nauyin renon waɗannan yara. Ko da yake waɗannan iyaye aro na samun tallafi daga hukuma amma duk da haka hukumar na shimfiɗa musu tsauraran sharuɗɗa. Daga ciki kuwa dole ne a kullum ɗaya daga cikin ma´auratan dake renon yaran ya kasance a gida wato kenan ba zai iya yin wani aiki daban ba. Hakazalika dole ne kuma iyayen aron su kasance masu tsaukin lamarin waɗanda hukumar za ta iya juyasu yadda take so. Sabine Steinkühler ita ce jami´ar dake zaɓan iyalan da ake ba su nauyin kula da yara a nan Bonn ta yi bayani kamar haka.

“Idan wasu iyaye suka yi rajista da mu, muna kai musu ziyara a gidajensu domin mu tabbatar da cewa suna da isasshen wuri kuma wanda ya dace na ba su renon yara. Muna gabatar da kwasa-kwasai da yawa ga iyalai masu sha´awar aikin renon yara. Muna nuna musu abubuwan da ya kamata su yi lokacin da yaran ke hannunsu da kuma yadda za su shirya wajen yin bankwana da yaran.”

Bankwana da yaran wani batu ne da a wasu lokutan yake zamewa Marlies Muckmalschi dole ta yi. Ta ce idan kan san cewa yaro zai faɗa hannun kirki ne yin bankwana da shi ba abu ne mai wuya ba. Sau ɗaya ne kawai ba ta yi bankwana da ɗaya daga cikin yaran da ake ba ta nauyin kula da su ba. Wato Daniela dake zama ƙaramar yarinyarta a yanzu. Tun dai Daniela ta na jinjira aka sa ta hannun wannan talika kuma sai baya watanni shida sannan ta yi dariya a karin farko.

“Wannan yarinyar yanzu ta zama ta mu. Domin bayan watanni shida lokacin da ya kamata mahaifiyarta ta ɗauke ta, sai ta nuna cewa ba ta da shirin sake ɗaukarta, saboda haka sai muka ɗauke ta ta zama ta mu.”

Yanzu haka dai Daniela ta cika shekaru uku kuma ta fara zuwa makarantar nasare. Sai jefi-jefi ne take ganin mahaifiyarta, amma Mama ta ke kiran Marlies Muckmaschli.