Mutane kussan 90 sun rasa rayuka a haɗarin jirgin sama a ƙasar Thailand. | Labarai | DW | 16.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane kussan 90 sun rasa rayuka a haɗarin jirgin sama a ƙasar Thailand.

Hukumomin Thailand ,sun bada ƙarin haske, a game da mutanen da su ka rasa rayuka a sakamakon haɗarin jirgin saman da ya abku yau lahadi, a filin saukar jiragen sama na tsibirin Phuket, da me kudancin ƙasar.

Baki ɗaya mutane 88 su ka rasa rayuka, mafi yawan su yan awan buɗe ido, daga ƙasashe daban-daban na dunia.

Jirgin yayi salla daka, a lokacin da ya ke ƙoƙarin sauka, ɗauke da mutane 123, wanda su ka hada da baƙi 78.

Binciken gawawakinda aka yi ya nunar da cewa daga wanda su ka mutum akwai yan ƙasar Thailand 14, yan Britania 8, 5 yan ƙasar Iran, 4 na Jamus sai kum a2 yan asulin Australiya.

Jirgin ya rabu gida 2, bayan ya dungura goshin sa ƙasa, inda kuma a nan take ya kama da wuta.

Shugabanin kampanin One-Two –Go, da ya malaki wannan jirgi, ya ce jamai´an tsaro za su fara bincike tun daga gobe, domin ida tantance mussababin haɗarin.