1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane fiye da 50 sun rasa rayuka a hare-haren da Isra´ila ta kai a garin Kana dake kudancin Labanon

July 30, 2006
https://p.dw.com/p/Buod

Dakarun Isra´ila da na Hezbollah na ci gaba da masanyar wuta a kudancin Labanon.

Da sanhin sahiyar yau rundunar Isra´ila ta yi ruwan bama bamai ta sararain samaniya, a kan garin Kana,inda a ƙalla mutane 50, take,mafi yawan su ƙananan yara, su ka rasa rayuka.

Daga sassa daban-daban na dunia ana ci gaba da Allah wadai da wannan harin na Isra´ila.

A birnin Beyruth dubun dubunnan jama´a, su ka shirya tafiyar jerin gwano, domin yin Allah wadai ga harin.

Praministan Labanon Fouad Siniora, ya gabata da jawabi bayan harin, inda ya ya bukaci tsagaita wuta.

A sakamakon halin baƙin ciki da Labanon ta shiga, sakaratiyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice,da ke ziyara a yankin gabas ta tsakiya,ta fasa kai ziyara da ta shirya, zuwa Labanon a yau ɗin nan.

Daga yankuna daban-daban na ƙasashen turai da na Larabawa, gwamnatoci sun yi ta hiddo sanarwoyin tofin Allah tsine, ga hare haren na yau.

A nata ɓangare,gwamnatin Iran, cewa ta yi harin na Kana bai ba ta mamaki ba, domin shine babban sakamakon da Condoleesa Rice, ta je nema Isra´ila, a ziyara aikin da ta fara jiya.

Duk da wannan Allah wadai, daga dunia, Praministan Isra´ila Ehud Olmert, yayi kunnen uwar shegu, ya kuma yin alkawarin ci gaba da kai hare haren, har sai Hezbollah ta bada kai ,bori ya hau.