Mutane fiye da 20 suka halaka sakamakon guguwa mai karfi a turai | Labarai | DW | 19.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane fiye da 20 suka halaka sakamakon guguwa mai karfi a turai

Daya daga cikin guguwa mafi karfi data taba ratsa arewacin turai ta halaka mutane akalla 27, 7 kuma daga cikinsu anan Jamus.

Sauran kuma a kasashen Burtaniya da Faransa da netherlands.

Guguwar dake da karfin gudun kilomita 190 cikin saa guda ta haddasa matsaloli na zirga zirgan motoci a yankunan data ratsa,kusan zaa iya cewa harkokin zirga zirag na jiragen kasa a Jamus da Holland sun dakatar da aiyukansu baki daya,a filin jirgin saman Frankfurt an soke kusan yawancin tashi da saukar jirage.

Guguwar dai ta tumbuke bishiyoyi, da lalata gine gine da dama tare da haddasa ambaliyar ruwa a wurare da dama.