1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu a wani hari a Kabul

Gazali Abdou Tasawa
May 31, 2017

KImanin mutane 80 ne suka mutu a yayin da wasu sama da 350 suka ji rauni a sakamakon tashin wani bam da sanyin safiyar wannan Laraba a birnin kabul na Afghanistan. 

https://p.dw.com/p/2dsVb
Afghanistan Explosion in Kabul
Hoto: Getty Images/AFP/S. Marai

Rahotanni daga Afghanistan na cewa akalla mutane 80 ne suka mutu a yayin da wasu sama da 350 suka ji rauni a sakamakon tashin wani bam tun da sanyin safiyar wannan Laraba a birnin kabul. Ma'aikatar harkoki wajen Jamus ta bayyana cewar jami'an ofishin jakadancinta da ke babban birnin na Afghanistan na daga cikin wadanda suka samu raunuka

Kakakin ofishin ministan cikin gida na kasar Najib Danish wanda ya tabbatar da afkuwar lamarin ya ce wata mota ce da aka dana wa bam ta tarwatse, kuma lamarin da ya wakana ne a unguwar da ke da akwai ofisoshin jakdancin kasashen ketare a birnin na Kabul. Kuma har harin ya shafi ofishin jakdancin Faransa a birnin na Kabul. .

Sai dai har kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, kana suma hukumomin kasar ba su bayar da cikakken bayani ba kan takamaiman abin da aka hara.