1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane da dama sun mutu a harin Boko Haram

April 2, 2018

Bayanan da ke fitowa daga birnin Maiduguri a Najeriya, na cewa an kwashe daren Litinin ana jin musayar harbe-harbe tare da fashe-fashe a wajen birnin inda aka yi asarar rayuka sama da 15.

https://p.dw.com/p/2vMSs
Nigeria Soldat
Dakarun Najeriya a bakin aiki wajen birnin MaiduguriHoto: picture-alliance/AP Photo/L. Oyekanmi

Rahotanni daga Najeriya na cewa an yi ta jin karar harbe-harbe da wasu fashe-fashe a birnin Maiduguri da ke yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Bayanai sun ce sojoji ne suka sha artabu da wasu mayakan kungiyar Boko Haram da suka yi kokarin shiga birnin kuma an yi asarar rayuka sama da 15 yayin da wasu 84 suka jikkata. Ya zuwa yanzu dai bayanai sun ce sojojin sun sha karfin mayakan tare da hana su cimma burinsu na shiga garin. Shiga Maidugurin dai wani babban burin mayakan ne tsawon lokaci. Sai dai ba a kai ga sanin adadin wadanda musayar wutar ta shafa ba.

Wannan lamari na zuwa ne dai-dai lokacin da gwamnatin Najeriyar ke cewa ana kan shirin sulhu da mayakan na Boko Haram da suka dauki shekaru akalla tara suna kashe-kashe. Ko a ranar Juma'ar da ta gabata ma an kaddamar da wasu hare-haren kunar bakin-wake a yankin Muna Garaj da ke Maiduguri, inda mahara uku suka mutu wasu mazauna yankin kuma suka jikkata.