Mutane da dama sun hallaka bayan ruftawar wata coci a Najeriya | Labarai | DW | 11.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun hallaka bayan ruftawar wata coci a Najeriya

Rahotanni daga Najeriya na nuni da cewa mutane da dama sun hallaka sakamakon ruftawar ginin wata coci a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

Nigeria Einsturz Kirche (picture alliance / dpa)

Ruftawar ginin coci ta hallaka mutane da dama a jihar Akwa Ibom a Najeriya

A ranar Asabar 10 ga wannan wata na Disamba da muke ciki ne dai wannan al'amari ya afku, inda har kawo yanzu babau takamaiman alkalumma na asarar rayukan da aka tafka sakamakon rahotanni mabanbanta da ake samu daga bangaren hukumomi da kuma kafafen yada labaran kasar. A yayin da a hannu guda jami'an 'yan sanda ke nuni da cewa mutane 27 ne suka hallaka yayin da wasu 30 kuma suka jikkata a wannan coci, a daya hannun Hukumar bada Agajin Gagaggawa ta kasar NEMA na cewa mutane shida ne suka rasa rayukansu yayin da wasu 115 kuma suka jikkata, a wannan hadari na ruftawar da ginin cocin Reigners Bible Church International da ke a birnin Uyo. 

Daruruwan mutane ciki har da manyan baki da suka hadar da gwamnan jihar ta Akwa Ibom, Udom Emmanuel na cikin wannan gini da rufinsa ya rufta kan jama'a da ke ibada. Gwamnan da wasu manyan baki sun tsallake rijiya da baya, ya kuma bayyana lamarin a matsayin abu mara dadi da za su yi bincike a kai. Koda a shekara ta 2014 ma dai sai da wani gini mai hawa-hawa ya rufta kan wata majami'a ta All Nations a jihar Legas cibiyar kasuwancin Najeriyar, abin da ya yi sanadiyar asarar rayukan mutane 116, mafi akasari 'yan kasar Afirka ta Kudu. Masu aikin ceto dai na can na ci gaba da ganin sun ceto wadanda ke da sauran numfashi, wata kila a nan gaba ana iya samun cikakken adadin wadanda suka hallaka a wannan hari.