Mutane da dama sun hallaka a Siriya | Labarai | DW | 23.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane da dama sun hallaka a Siriya

Mutane sama da 100 ne suka rasa rayukansu sakamakon wasu jerin hare-haren bama-bamai da aka kai a yankunan da ke karkashin ikon gwamnatin kasar Siriya.

Sababbin hare-hare a Siriya

Sababbin hare-hare a Siriya

Masu fafutuka da kuma masu sanya idanu kan yakin na Siriya sun tabbatar da afkuwar harin, inda shugaban kungiyar kare hakkin dan Adam da ke sanya idanu a yakin na Siriya wadda ke da matsuguni a birnin London na kasar Birtaniya Rami Abdel Rahman ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA cewa sama da mutane 48 ne suka hallaka a yankin Tartus yayin da wasu 73 suka rasa rayukansu a Jableh duk kansu da ke wajen gundumar Latakia. Hare-haren dai an kai su ne a tashoshin ababen hawa daban-daban da ke wadannan birane da kamfanin rarraba hasken wutar lantarki da kuma mashigar sashen bada agajin gaggawa na babban asibiti da ke birnin Jableh. Tuni dai kungiyar 'yan ta'addan IS ta bayyana cewa ita ce ke da alhakin harin.