Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon tashin wani bam a birnin Bagadaza yau sa safen nan. | Labarai | DW | 30.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon tashin wani bam a birnin Bagadaza yau sa safen nan.

A ci gaba da haɓakar tashe-tashen hankulla a Iraqi, wani bam ya tashi yau safen nan a birnin Bagadaza, inda mutane biyu suka rasa rayukansu, sa’annan wasu 4 kuma suka ji rauni. Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta bayar ta ce an ta da bam ɗin ne a unguwar Sadr City, mai rinjayin mazauna ’yan ɗariƙar shi’iti.

Kafin tashin bam ɗin dai, sai da dakarun Amirka da sojojin Iraqin suka yi wa unguwar ƙawanya, bayan wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wani sojan Amirkan. A jiya lahadi, sai da ɗaruruwan mazauna unguwar Sadr City ɗin suka yi zanga-zangar nuna ɓacin ransu ga mamaye unguwar da dakarun Amirka suka yi, wai don gano ɗaya daga cikinsu da aka yi garkuwa da shi.