1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane biyu sun mutu a rikicin Bamenda

Mouhamadou Awal Balarabe
December 9, 2016

Wani sabon rikici da ya barke tsakanin 'yan kamaru da ke magana da Ingilishi da jami'an tsaro a Bamenda ya haddasa mutuwar mutane biyu zuwa hudu.Suna neman a sake rungumar tsarin tarayya maimakon Jamhuriya.

https://p.dw.com/p/2U3LT
Tshirt Francophonization
Hoto: Moki Kindzeka

Wata arangama tsakanin masu zanga-zanga da 'yan sandan kwantar da tarzoma ta haddasa mutuwar mutane akalla biyu a Bamenda, daya daga cikin biranen da ake amfani da Turancin Ingilishi a cikinsu a Kamaru. Wannan tashin hankalin ya faru ne tun a ranar Alhamis okacin da gungun matasa suka yi yunkurin tarwatsa gangamin da jam'iyyar RDPC ko CPDM da ke mulki ta shirya, da nufin kiran malamai da su kawo karshen yajin aikin da suke gudanarwa.

Tun dai makonni biyun da suka gabata ne lauyoyin da malaman makarantun yankin da ke amfani da Ingilishi suka tayar da kayar baya dangane da abin da suka kira "cin kashi da masu magana da Faransanci ke yi musu." Ko da a karshen wata Nuwamba ma dai sai da wani matashi ya rasa ransa a lokacin zanga-zangar neman mayar da kasar kan tsarin tarayya maimakon Jamhuriyar.

Kashi 20 daga cikin 100 na al'ummar Kamaru ne ke amfani da Ingilishi. sai dai kuma suna kokawa da mayar da su saniyar ware duk da cewar yankinsu ne ya kunshi arzikin man fetur da ke shigar wa gwamnatin kudin shiga.