Mutane biyu sun mutu a kuri´ar raba gardama a Demukiradiyyar Kongo | Labarai | DW | 18.12.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane biyu sun mutu a kuri´ar raba gardama a Demukiradiyyar Kongo

Mutane biyu sun rasu a wata turereniya da ta auku a tashoshin zabe a gabashin kasar JDK lokacin da mutane ke rige-rigen kada kuri´a a rumfunan zabe a wata kuri´ar raba gardama ta farko bayan yakin basasan kasar. Wani jami´in gwamnati ya ce an tattake wani jinjiri dan wata 4 da haihuwa har lahira lokacin da masu zabe ke ruguguwar kada kuri´a a wata rumfar zabe da ke Rutshuru mai tazarar kilomita 80 arewa da garin Goma. Jami´in ya ce mahaifiyarsa ce ta yar shi a lokacin ruguguwar. Wani jami´in MDD a garin Goma kuma yace an murkushe wata mata har lahira sakamakon wani turmutsumutsu a wata rumfar zaben. Kuri´ar raba gardamar akan daftarin kundin tsarin mulkin kasar ta kasance irinta ta farko cikin sama da shekaru 40 a JDK. Saboda yawan masu kada kuri´a, jami´an zabe a kasar sun ce zasu sake bude tashoshin zabe a ranar litinin don bawa sauran mutane damar kada ta su kuri´a.