Mutane biyar sun mutu cikin wani hari a Kamaru
September 20, 2015Hukumomin sojin ƙasar Kamaru sun tabbatar da mutuwar mutane biyar da suka haɗa da ɗan sanda guda a cikin wasu tagwayen hare-haren da wasu 'yan ƙunar baƙin wake suka kai da sanhin safiyar wannan Lahadi a unguwar Galdi ta birnin Mora na yankin arewacin ƙasar kusa da kan iyaka da Najeriya.Hukumomin tsaron ƙasar ta Kamaru sun ce wasu ƙananan yara ne dai macce da namiji suka kai wannan hari inda suka tayar da bam ɗin da ke jikinsu a lokacin da wani ɗan sanda ya nemi ya bincikesu a kan hanyarsu ta shiga birnin na Mora wanda kasuwarsa ke ci ranar Lahadin nan inda dubban jama'a suka taru domin sayen raguna Sallahlayya.
Hukumomin sojin ƙasar ta Kamaru sun ce tuni suka aika da masu bincike a gurin da aka kai harin a yayin da a share daya jami'an tsaro suka shiga farautar wasu mutanen ukku da ke tare da masu ƙunar bakin waken, da suka tsere bayan abkuwar lamarin.