1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane biyar sun muta a wani hari a Kamaru

Mouhamadou Awal Balarabe
February 22, 2018

Mayakan Boko Haram sun kai wani sabon hari a garin Assigashia na arewacin kamaru, lamarin da ya salwantar da rayukansu fararen hula tare da jikata karin wasu.

https://p.dw.com/p/2t8lD
Karte Kamerun Extrême-Nord Englisch

Wasu fararen hula biyar sun rasa rayukansu a wani harin da mayakan Boko Haram suka kaddamar a garin Assigashia a kuri'ar Arewacin kamaru. Mahukuntan kasar da suka bada wannan sanarwa a wannan Alhamis sun bayyana cewar harin ya wakana ne a daren Talata zuwa Laraba kuma ya jikata wasu karin mutane biyar.

Dama dai garin Assigashia da ke kan iyakar Kamaru da Najeriya ya saba fusakntar hare-haren 'yan Boko Haram, inda ko a watan Janairu, mutum daya ya rasa ransa a makamancin wannan hari. Kungiyar International Crisis Group ta nunar da cewa mutane dubu biyu ne suka rasa rayukansu a Arewacin kamaru tun bayan da ta shiga cikin jerin kasashe da Boko Haram ke kai hare-hare a 2014.

A shekara ta 2009 wato shekaru taran da suka gabata ne kungiyar Boko Haram ta fara gagwarmaya da makamai a kasashen Najeriya da Chadi da Kamaru da Jamhuriyar Nijar, lamarin da ya haddassa mutuwar mutane dubu 20 ya zuwa yanzu.