1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 9 sun mutu a harin bam a Turkiyya

November 4, 2016

A cigaba da dambarwar rikici a Turkiyya wani harin bam ya halaka mutane tara a Diyarbakir a daidai lokacin da gwamatin ta yi dirar mikiya a kan wasu shugabanin adawa.

https://p.dw.com/p/2SBvg
Türkei Anschlag in Diyarbakir
Hoto: Reuters/Ihlas News Agency

Fashewar bam din ya faru ne a Diyarbakir 'yan sa'oi bayan hukumomi sun tsare yan majalisar dokoki akalla su 12 na Jam'iyyar adawa ta HDP. Akalla mutane tara suka hallaka wasu da dama kuma suka sami raunuka.Ministan shari'a Bekir Bozdag ya ce wadanda suka sami raunuka sun hada da 'yan sanda da kuma fararen hula.Turkiyya dai ta daure shugabanni biyu na babbar Jam'iyyar adawa ta Kurdawa da kuma wasu yan majalisar dokoki na bangaren adawar a wani matakin dirar mikiya da ba'a saba gani ba. Wata kotu ce dai a birnin Diyarbakir ta bada umarnin tsare shugabanin jam'iyyar adawar ta HDP a gidan wakafi zuwa lokacin da za'a yi musu shari'a. Amirka da kungiyar taryyar turai sun yi Allah wadai da kamen da ke zama wani sabon salon dirar mikiya da gwamnatin ta kaddamar karkashin dokar ta baci da ta kafa bayan juyin mulkin 15 ga watan yuli da bai yi nasara ba. Firaministan Turkiyya Binali Yildrim wanda ya dora alhakin harin bam din akan yan PKK, yace sun sake nuna irin mummunar halayyarsu.