Mutane 9 suka halaka cikin hari kan Agip a Najeriya | Labarai | DW | 24.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 9 suka halaka cikin hari kan Agip a Najeriya

Wasu yan bindiga sun kai hari kan ofisoshin kanfannin man fetur na Agip mallakar kasar Italiya a kudancin Najeriya,wanda ya janyo musayar wuta da tayi sanadiyar mutuwar mutane 9.

Wani jamiim kanfanin na Agip daya nemi a boye sunansa yace,yan bindigan sun kai harin ne a ofishinsu dake birnin Fatakwal,yan sanda 8 da wani farar hula maaikatcin kanfanin d ba suka halaka.

Wadanda suka kai harin sun sace kudi,inji jamiin wanda yace yana ganin yan fashi ne ba yan kungiyar gani kashe ni ba,kodayake sunyi barazanar kara kaimin kai hare hare kan kanfanonin mai na yankin.