1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 86 sun mutu a rikicin jihar Filato

Salissou Boukari
June 25, 2018

Rahotanni daga Tarayyar Najeriya na cewa mutane sama da 86 aka kiyasta cewa sun mutu sakamakon wani hari da ake zargin wasu makiyaya sun kai wa wasu manoma a yankin jihar Filato.

https://p.dw.com/p/30Ctb
NO FLASH Religiös motivierte Unruhen in Zentralnigeria
Hoto: picture-alliance/dpa

Da yake magana kan wannan batu Kwamishinan 'yan sanda na jihar Filato Undie Adie ya ce wani bincike da aka gudanar a ranar Asabar a garuruwan da ke yankin Barakin Ladi a gabashin jihar ta Filato, ya bada damar kiyasta mutane 86 da aka kashe, inda ya ce wasu mutane shida kuma sun samu raunuka yayin arangamar, sannan an kona gidaje 50.

A jiya Lahadi dai an kafa dokar hana zirga-zirga a yankin da ya dade yana fama da rikici tun yau da 'yan kwanaki, inda makiyaya da manona ke zaman doya da manja.

A jiya Lahadi ma matasan kabilar Birom sun kafa shingaye a kan hanya tsakanin Jos babban birnin jihar ta Filato da Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya domin kai hari ga masu motoci da ke kama da Fulani, da muka Musulmai, kamar yadda wasu matafiya da suka tsira da rayukansu suka sanar.