Mutane 8 sun rasa rayuka a rikicin gonnaki a iyakokin Mali da Burkina Faso | Labarai | DW | 04.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 8 sun rasa rayuka a rikicin gonnaki a iyakokin Mali da Burkina Faso

Rikici tsakanin manoma a iyakar Mali da Burkina Faso, ya hadasa mutuwar mutane 8, daga ɓangaren Burkina faso.

Wannan sanarwa, ta hito daga opishin ministan cikin gida na Ouagadougou.

Faɗace faɗacen, sun wakana tsakanin mazauna ƙauyen Ouoronkuy a arewa maso yammacin Burkina Faso, da mutanen garin Waniyen na ƙasar Mali.

Hasuni ya faru, sanadiyar gonnakin noma.

Sanarwar ta Ministan cikin gidan Burkina faso, ta bayana takaici a game da wannan faɗa, ta la´akari da kyaukayawar alaƙa, da cuɗe ni in cuɗe ka,da ta haɗa ƙasashen 2, da ke maƙwabtataka da juna.

Sannan magabatan Mali da na Burkina Faso, sun alƙwarta ɗaukar mattakan da su ka dace, domin maido doka da oda a yankin da abun ya faru.

Kazalika sun bayana cewar wannan rikici, ba zai shafi kaukawar danganta ba, a tsakanin su.