1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutane 700 sun kubuta a hannun Boko Haram

Abdul-raheem Hassan
January 2, 2018

Sama da mutane 700 da kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a Najeriya, sun samu damar tserewa daga hannun kungiyar kwanaki kalilan bayan da suka shiga hannu.

https://p.dw.com/p/2qCTa
US-Fotojournalistin Stephanie Sinclair
Hoto: Stephanie Sinclair

Rundunar sojin Najeriya ta ce yawancin wadanda kungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da su a matsayin bayi, masunta ne tare da iyalansu. Babu karin bayani kan lokacin da aka yi garkuwa da mutanen, amma rundunar ta yabawa dakarunta na kubutar da masuntan bayan kaddamar da farmaki kan mayakan a kusa da yakin tafkin Chadi. Kungiyar Boko Haram ta dau lokci tana barazana ga rayuwar al'umma a arewa maso gabashin Najeriya da wasu kasashe makota, Inda aka yi kiyasin kungiyar ta kashe akalla mutane dubu 20,000 kana wasu da dama suka rasa matsugunansu.