Mutane 7 sun rasu sakamakon wani tashin hankali a Gaza | Labarai | DW | 13.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 7 sun rasu sakamakon wani tashin hankali a Gaza

Akalla mutane 7 ´yan sandan Hamas suka kashe a Gaza a lokacin da magoya bayan kungiyar Fatah su kimanin dubu 200 suka hallara don girmama shugaban Falasdinawa Yasser Arafat wanda ya rasu shekaru 3 da suka wuce. Tun a cikin watan yunin wannan shekara Gaza ya koma karkashin ikon kungiyar Hamas wadda ke adawa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas wanda ya yi tir da kashe kashe a wani jawabi da yayi ta gidan telebijin. Abbas ya bayyana kisan da cewa aikin ´yan tawaye ne. Shugaban na Falasdinawa ya ba da umarnin zaman makoki na kwanaki 3 don juyayin wadanda aka kashen. Majiyoyin asibiti sun ce mutane sama da 100 sun samu raunuka a hargitsi da ya barke tsakanin mayakan kungiyoyin biyu da ba sa ga maciji da juna, lokacin gangamin na ´ya´yan kungiyar Fatah.