Mutane 60 sun rasu a rushewar rufin ginin wata cibiyar kasuwanci a Poland | Labarai | DW | 29.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 60 sun rasu a rushewar rufin ginin wata cibiyar kasuwanci a Poland

Yawan wadanda suka mutu sakamakon ruftawar rufin wani ginin kasuwar baje koli a kusa da garin Kattowitz dake kudancin kasar Poland yanzu ya kai mutum 60 yayin kimanin 130 suka samu raunuka. Rahotanni daga yankin sun ce yawan wadanda suka rasu zai haura haka, domin har yanzu akwai mutane a karkashin buragusan ginin, kuma har yanzu ma´aikatan ceto ba su kai garesu ba. Daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su akwai Jamusawa da kuma wasu ´yan kasashen Turai da dama. Bisa ga dukkan alamu nauyin dusar kankara da ta zuba a cikin kwanakin nan sakamakon sanyin hunturu, ya janyo ruftawar rufin ginin. Sama da mutane dubu daya ke cikin ginin lokacin da hadarin ya auku. A halin da ake ciki shugaban Poland Lech Kaczynski ya ba da sanarwar zaman makoki a fadin kasar baki daya.