Mutane 5 sun rasu a wani rikicin siyasa a birnin Addis Ababa | Labarai | DW | 01.11.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mutane 5 sun rasu a wani rikicin siyasa a birnin Addis Ababa

´Yan sandan kwantar da tarzoma sun yi arangama da magoya bayan ´yan adawa a babban birnin kasar Habasha, inda suka harbe mutum biyar har lahira sannan 18 suka jikata, a wani sabon rikici da ya barke sakamakon zaben da aka gudanar ranar 15 ga watan mayu. Ma´aikatan kiwon lafiya sun ce an harbe mutanen ne a kirji yayin da aka raunata wasu a kafa da hannu. Wani wakilin kamfanin dillancin labarun Associated Press ya ce ya ga lokacin da motocin asibiti na kungiyar Red Cross suka kai mutane biyar jina-jana asibitin Black Lion dake birni Addis Ababa. Daga cikin mutane akwai mace daya da aka harbe ta a fuska da wani mutum da aka harbe shi a baya. A asibitin wasu daga cikinsu suka cika. Wannan tashin hankalin ya auku ne kwana daya bayan da ´yan sanda suka kame kuma karbe lasinsin direboin tasi guda 30 da suka shiga cikin sabuwar zanga-zangar nuna adawa da sakamakon zaben. ´Yan sanda sun halaka mutane 42 a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben a cikin watan yuni.